Ma’aikatar lafiya ta kasar Libiyan ce ta sanar da hakan inda ta ce tuni aka garzaya da wadanda suka sami raunukan zuwa wasu asibitoci 5 yankin don yi musu magani.
Gwamnatin kasar dai ta zargi Janar Haftar, wanda ya taka rawa wajen kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi da kokarin shirya juyin mulki da kifar da gwamnatin tana mai shan alwashin kawo karshen wannan rikicin.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin gwamnati, majalisa da sojojin kasar Libiyan suka fitar sun sha alwashin ci gaba da fada da masu tada fitinar suna masu sanar da hana tashi da kuma shawagin duk wani jirgi a garin na Bengazi da barazanar kakkabo duk wani jirgin da aka ganshi a sararin samaniyar. Wannan barazanar dai ta biyo bayan rahotannin da suke cewa dakarun tsohon janar din sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai hare-hare.ABNA